IQNA

An Bude Cibiyar Kasa Da Kasa Ta yaki Da Tsattsauran Ra’ayi A Syria

23:59 - May 21, 2019
Lambar Labari: 3483663
Bangaren kasa da kasa, an bude cibiyar kasa da kasa ta yaki da tsatsauran ra’ayin addini a kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran SANA ya bayar da rahoton cewa, daga cikin wadanda suka jagoranci bude cibiyar har da shuagabn kasa ta Syria, da Sheikh Badruudin Hassun babban mufti na kasar, Muhammad Adnan Abdulsattar ministan ma’aikatar kula da harkokin addini, Muhammad Tafiq Albudi, shugaban majalisar malaman yankin Sham.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, shugaban Syria Bashar Assad ya bayyana cewa, babbar manufar bude wannan cibiya, wadda ta hada manyan malamai da masana daga ciki da wajen kasa Syria, shi ne samar da hanyoyi na yaki da tsatsauran ra’ayi a ilmance.

Ya ce babu wani abu tsatsauran ra’ayia  addini, domin kuwa musulunci da dukkanin addinai da aka saukar daga sama, suna magana ne da dan a hankalce kuma a ilamnce, ba ta hanyar dabbanci da rashin hankali da jahilci ba.

Shugaba Assad ya kara da cewa, nauyi ne da ya rataya kan dukkanin malamai na addini, da su wayar da kan al’umma kan hakikanin koyarwar addini, musamman wadanda ake yaudara saboda jahilcinsu da addini, inda ya ce akidar wahabiyanci ta taka gagarumar rawa wajen haifar da tsatsauran ra’ayi, wada kan kai jahilai fadawa cikin ayyukan ta’addanci.

3813408

 

captcha