IQNA

Bukin Bude gasar Kur'ani ta Duniya A kasar Aljeriya

23:58 - May 26, 2019
Lambar Labari: 3483676
An bude babbar gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a kowace shekara a kasar Aljeriya, tare da halartar wakilan kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

Shafin yada labarai na Alnahar online ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da taron bude babbar gasar kur’ani ta duniya a birnin Aljiers fadar mulkin kasar Aljeriya, tare da halatar manyan jami’an gwamnatin kasar, da kuma wakilai daga kashe 50.

Ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na kasar Aljeriya Yusuf Bilmahdi ne ya jagoranci bude taron, tare da halartar wasu daga cikin ministocin kasar, inda da farko aka fara da yin addu’a ga musulmin kasar New Zeland da suka rasa rayukansu a hare-haren ta’addancin da aka kai musu a cikin masallaci.

Gasar dai kamar yadda aka saba ta kan hada dukkanin bangarorin da ake gudanar da gasa a kansu, haka nan kuma manyan alkalan gasar kur’ani na duniya guda shida za su yi alkalanci a gasar, wadda ita ce gasar kur’ani ta biyu mafi girma da ake gudanarwa a kasashen Afirka bayan gasar kasar Masar.

Ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Aljeriya ta sanar da cewa, za a dauki tsawon mako guda ana gudanar da wannan gasa.

Mohammad Hussain Behzadfar mahardacin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran ne zai wakilci kasarsa a gasar.

 

 

 

3814706

 

captcha