IQNA

Sakon Rauhani Na Taya Shugabannin Musulmi Murnar Sallah

23:49 - June 05, 2019
Lambar Labari: 3483711
Shugaba Rauhani na Iran ya aike da sakonni zuwa ga shugabannin kasashe daban-daban na musulmi, domin taya su murnar salla, da kuma yi musu fata alhairi da dukkanin al’ummomin kasashensu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na ofishin shugaban kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya shugaba Rauhani ya aike da sakonni na taya murnar salla karama ga dukkanin shugabani na kasashen musulmi, inda ya yi fatan wanann idi ya zama mai albarka ga dukaknin al’ummomin muusmi da ma al’ummomin duniya baki daya.

Haka nan a cikin sakon nasa, shugaba Rauhani ya kirayi sauran takwarorinsana kasashen musulmi, da su kara hada karfi da karfe a matsayinsu na al’umma guda mai bin addinin muslucni, domin kawo fahimtar juna da zaman a lafiya tsakanin al’ummar musulmi.

Kamar yadda kuma ya yi fatan Allah ya karbi dukkanin ayyukan ibada da musulmi suka yi cikin watan mai alfarma, kuma ya kawo musu ci gaba da arziki da kwanciyar hankali a kasashensu, da ma duniya baki daya.

3817256

 

 

 

captcha