IQNA

22:53 - June 19, 2019
Lambar Labari: 3483753
Bangaren kasa da kasa, an harba wani makami ma linzamia  kusa da wani kamfanin na Amurka  a garin Basara na kasar Iraki.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, tashar sky News ta bayar da rahoton cewa,  wani sabon labara makamai masu linzami akalla gada ne ya fadi suka da sansanin sojojin kasar Amurka da ke birnin Musil na arewacin kasar Iraqi a jiya Talata.

Tashar ta bayyana cewa makaman samfurin katusha, kirar cikin gida ne sannan an cilla shi ne daga yammacin Musli a bangaren tekun Tigris, Makamin ya sauka akan ginin tsohuwar fadar shugaban kasa.

Shi kuwa Kwamanda mai kula da ayyukan soja a yankin ya bayyana cewa; Makamin ya fadi ne a wani sararin subuhana, ba tare da ya haddasa wata barna ba.

Bugu da kari, kwamandan sojan na yankin Neinevah ya tabbatar da cewa; Sun ci gaba da sa ido akan dukkanin abubuwan da suke faruwa, kuma ya zuwa yanzu babu wata matsala.

A ranar jum’ar da ta gabata ma dai wasu mutanen da ba a kai ga tantance ko su wanene ba, sun harba wasu makaman roka uku akan sansanin sojan sama dake arewa da birnin Bagadaza, inda sojojin Amurka suke bayar da horo.

Majiyar tsaro ta kasar Irakin ta tabbatar da cewa; Harin da aka kai akan sansanin sojan sama na Balad, mai nisan kilo mita satin da hudu  daga arewacin Masar, ya haddasa tashin gobara a cikin dajin dake yankin.

 

3820595

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Balad ، Basara
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: