IQNA

za A Koma Kan Teburin Tattaunawa A Sudan

23:58 - June 22, 2019
Lambar Labari: 3483762
Bangaren kasa kasa, 'yan siyasa da farar hula sun amince da shawarwarin da Habasha ta gabatar dangane da kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani na hadin gwiwa da suka fitar, bangarorin siyasa na kasar Sudan gami da sauran ‘yan farar hula masu fafutuka, sun amince da shawarwarin da Habasha ta gabatar, da nufin kawo karshen rikicin da kasar ta fada a cikinsa.

Bayanin ya ce shawarwarin na Habashasun hada da kafa gwamnatin rikon kwarya, wadda wata majalisa ta musamman za ta jagoranta, majalisar kuma za ta kunshi mambobi 15, da za su hada da sojoji 8 da kuma fararen hula 8 da za su hada da ‘yan siyasa da sauran bangarorin farar hula.

Bayan nan kuma za a zabi wani mutum guda wanda baya ko daya daga cikin bangarorin biyu, wanda dukkanin bangarorin biyu za su cimma daidaito a kansa domin ya jagoranci majalisar, wanda kuma shugabancin zai zama na karba-karba ne.

A yau Asabar ne ake sa ran bangarorin siyasar za su mika bayaninsu a hukumance ga bangaren masu shiga tsakani na kasar Habasha.

3821452

 

 

captcha