Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an baiwa Misam lakabin yarinya mafi karancin shekaru da ta hardae kur'ani a hadaddiyar daular larabawa.
Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa, diyarta mai shekaru shida har yanzu bata zuwa makarata ba, kuma ta fara hardar kur'ani ne tun tana da shekaru uku.
Ta e diyarta ta shiga gasar kur'ani a ta sheikh Zaid kuma ta zo matsayi na bakawai, inda a ahalin yanzu kuma ta kammala hardar kur'ani baki daya tana da shekaru shida a duniya.