IQNA

Gwamnatin saudiyya Na Da Hannu A Kisan Khashoggi

14:52 - June 27, 2019
Lambar Labari: 3483777
Babbar jami’ar majalisar dinkin duniya mai bincike kan kisan Khashoggi ta kara tabbatar da cewa gidan sarautar Saudiyya na da hannu a cikin wannan kisan gilla.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne babbar jami’ar majalisar dinkin duniya mai jagorantar bincike kan kisan dan jaridar nan Kamal Khashoggi Angen Callamard ta gabatar da rahotonta wanda ta harhada tare da tawagarta, bayan gudanar da binciken kwakwaf na tsawon watanni kan kisan Khashoggi.

A cikin rahoton Callamard ta bayyana cewa, dukkanin alamu sun tabbatar da cewa kisan Khashoggi wania bu ne da aka riga aka shirya shi, kuma a gidan sarautar Saudiyya ne aka shirya wanann kisan gilla, a kan haka dole ne a binciki yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman kan batun wannan kisa.

A cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ce dai aka yi wad an jaridar na kasar Saudiyya mai adawa da wasu manufofin Muhammad Bin salman kisan gilla a cikin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul na kasar Turkiya, inda aka daddatsa shi da zarto amia iki da wutar lantarki, daga bisani kuma aka sanya sanadarin acid aka narkarkar da gawarsa.

Daga farko dai Saudiyya ta musunta faruwar lamarin, bayan tabbatar da dalilai na hotunan da kamarori suka dauka, ta amince da faruwar lamarin bayan shudewar kwanaki goma sha tara, amma ta dora laifin ne kawai a akn wadanda suka aiwatar da kisan.

 

3822750

 

captcha