IQNA

Daesh Ta Dauki Nauyin Harin Ta’addancin Tunis

14:40 - June 28, 2019
Lambar Labari: 3483781
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar ‘yan ta’addan Daesh ta dauki nauyin harin ta’addancin da aka kai jiya a birnin Tunis na kasar Tunisia.

Shafin yada labarai na tashar Euro News ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta saka a shafinta an yanar gizo, kungiyar daesh ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin harin ta’addancin da aka kai jiya Alhamis a birnin fadar mulkin kasar Tunisia.

Harin na jiya dai ya zo ne bayan da wani dan ta’adda  ya tarwatsa kansa nisan mita 200 daga ofishin kadancin kasar Faransa da ke birnin na Tunis, inda jami’in tsaro guda ya rasa ransa wasu hudu kuam suka samu raunuka da suka hada da fararen hula biyu.

Bayan faruwar lamarin ba da jimawa ba wani dan ta’addan na biyu ya tarwatsa kansa kafin isa wurin da yake shirin kai harin, inda ya mutu shi kadai, ba tare da wani ya samu rauni ba.

Yusuf  Shahed Fira ministan kasar ta Tunisia ya bayyana cewa, hare-haren na ‘yan ta’addan Daesh alama ce ta gazawa, sakamakon raunin da suka yi, bayan da jami’an tsaron kasar suka murkushe su.

Kasar Tunisia dai ita ce kasa ta biyu bayan Saudiyya wajen yawan ‘yan ta’adda da suka tafi kasashen Iraki da Syria domin ayyukan ta’addan da sunan jihadi, inda a halin yanzu kasar ke fuskantar barazanar tsaro bayan dawowar wasu daga cikinsu.

3822938

 

 

 

captcha