IQNA

Daruruwan Irakawa Sun Yi Gangami A Gaban Ofishin Jakadancin Bahrain

14:46 - June 28, 2019
Lambar Labari: 3483783
Daruruwan Irakawa a cikin fushi sun gudanar da zanga-zanga da kuma yin gangami a gaban ofishin jakadancin kasar Bahrain da ke birnin Bagadaza domin nuna rashin amincewarsu da taron Manama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, kamfanin dilalncin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya ne daruruwan Irakawa a cikin fushi suka nufi ofishin jadakancin Bahrain da ke birnin Bagadaza, inda suka yi gangamin nuna rashin gamsuwarsu da taron da Amurka ta shirya a Bahrain kan Palestine.

Rahoton ya ce duk da shingayen tsaro da jami’an ‘yan sanda suka saka a kan hanyar da ke isa ofishin jakadancin na Bahrain, masu zanga-zangar sun samu isa wurin, inda suka sauke tutar Bahrain suka daga ta Palestine, da ta kasar Iraki, a lokaci guda kuma suka bankawa tutar Isra’ila wuta.

Jami’an tsaro sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu gangami, wadanda suke yin Allawadai da gwamnatin Bahrain, wadda ta dauki nauyin taron da Amurka da Isra’ila suka shirya  a kan Palestine, tare da hadin baki da kasashen Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa gami da Jordan.

Minstan harkokin cikin gida na Iraki ya ce sun kame mutane 54 daga cikin masu zanga-zangar, inda ya ce hakkin gwamnatin Iraki ne ta kare dukkanin ofisoshin kasashen duniya da suke cikin kasarta.

3822913

 

 

 

 

 

 

captcha