IQNA

Malaman Musulmi Na Duniya Sun Yi Allawadai Da Harin Tunisia

23:50 - June 29, 2019
Lambar Labari: 3483786
Kwamitin malaman addinin muslucni an duniya ya fitar da wani bayani wanda a cikinsa ya yi tir da Allawadai da harin da aka kai a kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa,a  cikin bayanin da kwamitin malaman addinin muslicni na duniya ya fitar kan batun harin na Tunisia ya bayyana shi da cewa ya yi hannun riga da koyarwar addini.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a  duk lokacin da aka samu wasu daga cikin masu ikirarin cewa su mabiya addinin musulunci ne, kuam suna aikata ayyukan ta’addanci da kisan bil adama, to ba su wakiltar addinin muslucni da wadannan ayyukan nasu.

A ranar Alhamis da ta gabata ce wasu ‘yan ta’adda biyu suka kai harin kuna bakin wake  a cikin birnin Tunis a kusa da ofishin kadancin kasar Faransa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’in tsaro guda tare da jikkatar wasu.

Bayan kai harin kungiyar ‘yan ta’adda ta daesh ta dauki alhakin kai wannan hari.

 

 

 

 

3823050

 

 

captcha