IQNA

Musulmin Ghana Sun Nuna Goyon Baya Ga Iran A Kan Barazanar Amurka

22:56 - June 30, 2019
Lambar Labari: 3483794
Bangaren kasa da kasa, gayammar kungiyoyin musulmi ta kasar Ghana ta nuna cikakken goyon bayanta ga Iran dangane da barazanar da Amurka ta yi wa kasar ta Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da suka ziyarci jakadan Iran a Ghana Ali Reza Faramarzi, tawagar gamayyar kungiyoyin musulmi a  kasar ta nuna cikakken goyon bayanta ga Iran dangane da barazanar da Amurka ta yi wa kasar ta Iran tare da jadda goyon bayansu ga matsayin da Iran din ta dauka  kan batun.

Hajji Abdul Mannan Abdulrahman shugaban gamayyar kungiyoyin musulmi a kasar ta Ghana ya bayyana cewa, abin da kasar Iran take fuskanta na matsin lamaba daga kasashe masu girman kai musamman Amurka, sakamako ne na tsayin dakan da take yi wajen kare martabar musulmia  duniya.

Ya ce kasar ta Iran ita kadai ce a halin yanzu take fitar da muuslmi kunya  a duniya, domin kuwa ba ta mika kai ga makiya addinin musulunc ba, kamar yadda kuma ba ta hada kai da su domina  cutar da musulmi.

Daga karshe ya yi kira ga sauran kasashe da su koyi da hakan, matukar dai suna son su wanzu cikin daukaka ta addini.

 

3823259

 

 

 

captcha