IQNA

Ayatollah Khamenei: Daga Karshe Falasinawa Da Duniyar Musulmi Za Su Yi Nasara

23:49 - July 22, 2019
Lambar Labari: 3483867
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyi Ali Khamenei jagoran juyin juya halin musulunci a Iran, a lokacin da yake ganawa daw ata tawaga ta kungiyar Hamas a yau ya bayyana cewa, batun falastine shi ne batu da yake gaban dukkanin musulmi a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatollah Sayyeed Ali Khamenei ya kara jaddada cewa batun al’ummar Falasdinu shi ne abin da ya fi damun al-ummar musulmi a halin yanzu, kuma ya bayyana haka ne a lokacin da wata tawaga ta Falasdinawa daga kungiyar Hamas ta ziyarce shi a gidansa a nan birnin Tehran.

Ayatollah Sayyeed Ali Khamenei, ya kara jaddada cewa ana samun nasara ne aka makiya ta hanyar gwagwarmaya, sannan ya ce, mu mun yi imani kan cewa, ko ba dade ko ba jima, nasara tana zuwa, domin alkawarin Allah ne, kuma Falasdinawa da musulmi ne za su sami nasara daga karshe.

A wani bangare na jawabinsa, jagoran ya ce, al’ummar Falasdinu sun fuskanci makirce-makirce da dama, a tsawon tarihin gwagwarmayan da suke yi da yahudawan sahyuniya, amma abin bakin ciki wasu kasashen Larabawa masu ha’inci, sun bi sahun Amurka da Isara’ila, wajen kulla wata sabuwar makarkashiya wadda ake kira “yerjejeniyar karni” a wannan lokaci.

Manufar hakan ita ce kawar da batun alummar Falasdinu sannan a hana su komawa kasarsu, da yardar Allah ba zasu sami nasara ba, domin  haka ku ta shi tsaye, kada ku yarda ku sayar da samuwarku da kudi.

Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa, goyon bayan da Jumhuriyar musulunci ta Iran ta ke bawa alummar Falasdinu, na daga cikin dalilan gaban da wasu manyan kasashen duniya suke da ita, amma duk da haka Iran ba zata taba janye goyon bayan da take bawa alummar Falasdinu ba, domin alamarin Falasdinu da birnin Qudu a wajenta, al’amarin Imani ne.

Iran tana goyon bayan al-ummar Falasdinu ne domin sauke nauyin da Allah ya dora mata, domin neman yardar Allah, sannan yin hakan ibada ce ga musulman kasar.

A wani wuri a cikin jawabin sa, Jagoran ya tabbatar da cewa, al’ummar Falasdinu tana samun nasara a gwagwarmayarta da yahudawan sahyudomin kuwa a cikin yan shekaru da suka gabata, ba sa da wani makami na kare kansu, inda banda  duwatsu da suke yin jifa da su, amma a halin yanzu suna da makamai da wasu kayayyakin aiki wadanda suke taimaka musu a  yakin da suke yi da gwamnatin yahudawa ‘yan mamaya.

Daga karshe jagoran ya kammala da cewa, shekaru arba’in da suka gabata, ba wanda yake tsammanin cewa za’a kafa jamhuriyar musulunci a Iran, sannan a maida ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Tehran ya zama ofishin jakadancin Falasdinu, amma hakan ya tabbata.

A kan haka dangane da nasarar al’ummar Falasdinu ma, hakan zai tabbata, matukar dukkanimmu mun yi aiki da abin da ya wajaba a kanmu, Sannan Allah ba zai taba saba alkawarin da ya yi wa muminai, na ba su nasara a kan makiyansu ba. 

 

3829099

 

captcha