Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron sun fara harbi akan masu Zanga-zangar a kusa da ginin sakateriyar gwmanatin tarayya dake birnin Abuja.
Majiyar harkar musulunci a Najeriya ta ambaci cewa; daga cikin wadanda aka harba din da akwai kananan yara da mata.
Tun bayan da aka fitar da wani rahoto na likitanci dake cewa lafiyar shugaban harkar musuluncin ta Iran ta kara tabarbarewa, mabiyansa suke gudanar da Zanga-zangar yin kira da a sake shi domin neman magani.