IQNA

Jehangiri: IranTana Kare Yarjejeniyar Nukiliya Ne Daidai Da yarjejeniyar

20:34 - July 29, 2019
Lambar Labari: 3483893
Bangaren siyasa, Mataimakin shugaban kasar Iran Ishaq Jehangiri ya bayyana cewa; dakatar da yin aiki da wani bangaren yarjejeniyar nukiliya da Iran ta yi, shi ma bangare ne na yin aiki da yarjejeniyar.

Jehangiri ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da shugaban kwamitin siyasa na jam’iyyar gurguzu da ke mulki a kasar China,aziyarar da yake gudanarwa a birnin Tehran.

Jehangiri ya ce dukkanin matakan da kasar Iran ta dauka dangane da batun yarjejeniyar nukiliya suna nan rubuce a cikin yarjejeniyar, kuma daukar wadanann sabbin matakai da ta yi zai taimaka wajen ceto yarjejeniyar.

Dangane da alaka tsakanin Iran da China kuwa, ya bayyana cewa alaka ce ta tarihi, wadda matsin lambar Amurka ba za ta iya yin tasiri a kanta ba, kuma a kullum wannan alaka tana ci gaba da kara bunkasa a ne a dukkanin bangarori.

Ya kara da cewa a cikin mako mai zuwa wata bababr tawaga daga kasar ta Iran za ta ziyarci kasar China, domin tattauna kan samar da wasu sabbin hanyoyi na mu’amalar bankunan kasashen biyu da kuma musayar kudade, wanda hakan zai kara taimaka ma dukkanin kasashen biyu wajen mu’amalarsu ta tattalin arziki da cinikayya.

3830903

 

captcha