IQNA

Ansarallah Ta Yi Na'am Da Matakin UAE Kan Yakin Yemen

23:50 - August 03, 2019
Lambar Labari: 3483909
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta yi na'am da sabon matakin da UAE ta dauka kan yakin kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Bukhaiti, kusa a kungiyar Ansarallah ta kasar yemen, kuma mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar ya bayyana cewa, suna maraba da matakin da UAE ta dauka na fara janyewa daga kasar Yemen.

Ya ce wanann mataki shi ne babban dalilin da ya sanya sojojin kasar da kuma dakarun sa kai na kungiyar da sauran bangarori a kasar suka dakatar da kai hare-haren ramuwar gayya kan hadaddiyar daular larabawa.

Ya kara da cewa, wannan mataki baya nufin cewa sojojin hadaddiyar daular larabawa da suka yi saura a cikin kasar Yemen suna cikin aminci ne, hakan ya danganta ne da matakai na gaba da UAE za ta dauka ne.

3831905

 

captcha