Kamfanin dillancin labaran iqna, Kotun koli da take a jahar Kaduna, a zaman da ta yi ayau Litinin ta yanke hukunci akan bayar da dama ga shugaban harkar musulunci a Najeriya, Sheikh zakzaky da ya tafi kasar India neman magani kamar yadda ya bukata
Sai dai shehun malamin da mai dakinsa, Zeenat ba su sami halartar zaman kotun na yau ba a lokaci da aka yanke hukunci.
Gabanin bude zaman shari’ar, an baza jami’an tsaro a kan muhimman titunan birnin Kaduna, An rufe babban titin Ahmadu Bello a daidai lokacin da ake dakon fara shari’ar.
Tun a shekarar dubu da sha biyar ne dai ake tsare da Sheikh Zakzaky bayan wani hari da sojojin kasar su ka kai wa gidansa a cikin birnin Zaria. A yayin wancan harin dai an kashe daruruwan magoya bayan Sheikh Zakzaky, kamar kuma yadda aka rusa ginin Husainiyya.