Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Almasirah cewa, a yau Juma’a wasu ma’aikatan kawancen Amurka da Isra’ila da saudiyya da ke kaddamar da hare-hare kan al’ummar Yemen, sun kashe Ibrahim Baduddin Alhuthi.
Ma’ikatar harkokin cikin gida ta kasar Yemen ta sana da cewa, an shiga bincike domin gano masu hannu a cikin lamarin.
Haka nan kuma tashar ta mika sakon ta’aziyya ga Sayyid Abdulmalik Badruddin Alhuthi jagoran kungiyarn Ansarallh.