IQNA

Barazanar Al-shabab Ga Makarantun Kasar Kenya

22:33 - August 13, 2019
Lambar Labari: 3483945
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ‘yan ta’addan Al-shabab ta yi mummunan tasiri ga tsarin karatu a yankin Madera na kasar Kenya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a ciki gaba da yunkurin da mayakan kungiyar ‘yan ta’addan kungiyar Alshabab masu dauke da akidar wahabiyanci suke na ganin sun rusa harkar ilimi a wasu yankuna na Kenya, a halin yanzu lamarin ilimi na neman tsayawa cak a yankin Mandera.

Bisa ga rahotannin da ma’aikatar ilimi ta kasar Kenya ta bayar, a cikin ‘yan shekarun nan sakamakon barazabnar da ‘yan ta’addan Alshahab suke yi ga daliban makarantu a yankin Mandera da ke kan iyakar kasar Kenya da Somalia, da dama daga cikin daliban sun kauracewa makarantunsu.

Kungiyar Alshabab wadda take dauke da akidar wahabiyanci, tana kafurta duk wani musulmi wanda bai shiga cikin kungiyar ba tare da halasta jininsa, kamar yadda take kallon wadanda ba musulmi a matsyin wadanda dole ne a zubar da jininsu.

 

3834646

 

 

 

captcha