IQNA

Ana Tayar Da Jijiyoyin Wuya Tsakanin Pakistan Da Indiya

23:52 - August 14, 2019
Lambar Labari: 3483948
Bangaren kasa da kasa, Imran Khan fira ministan Pakistan ya zargi Indiya da yunkurin aiwatar da ayyukan soji a Keshmir.

Kamfanin dillancin labaran iqna, gwamnatin kasar Pakistan ta fara jigilar makamai da kayakin yaki zuwa sansanin sojojin kasar na Skardu dake kan iyaka da kasar Indiya, wanda ake ganin alamu neda ke nuni da cewa mai yiwuwa yaki ya barke tsakaninta da kasar Indiya dangane da matsalar yankin Kashmir.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, jaridar “Asian News International “ ta nakalto wata majiyar gwamnatin kasar Indiya tana fadar haka, ta kuma kara da cewa an ga jiragen jigilar kayakin yaki da sojoji  yana jigilar kayayyakin yaki zuwa sansanin sojojin na Skardu kusa da lardin Ladakh na kasar Indiya.

Jaridar ta kara da cewa tun farkon watan Agustan da muke ciki ne gwamnatin kasar Indiya ta soke kwarya-kwaryan cin gashin kai wanda yakin na Kashmiir da ke karkashin kasar Indiya yake da shi.

Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun shiga yaki har sau uku kan mallakar yankin Kashmir wanda mafi yawan mazauna yankin musulmai ne.

Bayan soke kwarya-kwaryan cin gishin kai na yankin na Kashmir ne Firai Ministan kasar Pakistan Imran Khan ya bayyana cewa kasar Indiya wacce take da mabiya addinin hindu masu rinjaye a kasar, tana shirin yin kisan kiyashi wa musulman yankin Kashmir, kamar yadda sojojin Nazi suka yi a yakin duniya na biyu.

3835038

 

captcha