IQNA

Batun Tsaro A Najeriya Ya Dauki Hankulin Majalisar Dinkin Duniya

23:59 - September 03, 2019
Lambar Labari: 3484014
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta ce Matsalolin tsaro daban-daban a tarayyar Najeriya na bukatar daukar matakan gaggawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cewar majalisar dinkin duniya Matsalolin tsaro daban-daban a tarayyar Najeriya na bukatar daukar matakan gaggawa, domin kada ta zama matsala babba wacce zata shafi sauran kasashen yankin.
Agnes Callamard, jakadiya ta musamman ta majalisar dinkin duniya wacce ta ziyarci tarayyar ta Najeriya ce ta bayyana haka bayan ziyarar kwanaki 12 ta kai kasar.
Callamard ta bayyana haka a wani taron yan jarida da ta kira a birnin Abuja babban birnin tarayyar ta Najeriya a jiya Litinin.
Callamard ta ce, ma’aikatar shari’a sojoji da yansanda a kasar suna bukatar garan bawul saboda nuna karfi da iko da suka wuce kima da suke yi a lokacin suke gudanar da ayyukansu, wanda a wasu lokuta suke tunzura mutane zuwa tashin hankali.
Dangane da IMN ko kuma harka Islamiya a Nijeriya, Callamard ta ce gwamnatin kasar ta haramtata ne domin abinda take zata mambobin IMN zasu zama ne a gaba, amma ba abin da take yi a halin yanzu ba. Domin kuwa babu wata hujja da ta gani wadda ta take nuna cewa yayan wannan kungiyar suna dauke da makami wanda zai zama hatsari ga tsaron kasar.

3839615

 

 

captcha