Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Datch News cewa, magajin garin birnin Ayndhon John Garitsma ya sanar a jiya cewa, babu wani wanda yake da hakkin yin gangami na nuna kyama a ga musulmia kusa da wuraren ibadarsu.
Ya ce duk wanda yake son yin gangami domin bayyana wani ra’ayi nasa, to ya zo a gaban ofishin magajin garin birnin, domin hakan bai saba wa doka ba, amma yin gangami a gaban masallatan musulmi domin nuna rashin amincewa da akidarsu hakan ya sabawa doka.
Ya ce za su dauki dukaknin matakan da suka dace domin kare wuraren ibada na musulmi, tare da ladabtar da duk wanda ya sabawa wannan doka.
Kungiyar PEKIDA dai ta shahara a kasar Holland da ma wasu kasashen yankin wajen nuna tsananin kiyayya ga musulmi mazauna nahiyar turai.