IQNA

An shiga Mataki na Karshe a Gasar Kur’ani Ta Duniya A Makka

23:55 - September 08, 2019
Lambar Labari: 3484030
Bangaren kasa da kasa, an shiga mataki an karshe a gasar kur’ani mai tsarki da ke gudana a birnin Makka mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Alakhabr 24 cewa, a yau ne aka shiga mataki an karshe a gasar kur’ani mai tsarki da ke gudana a birnin Makka tare da halartar makaranta da mahardata 146 daga kashe 103 na duniya.

Mataki na karshe dai za a gudanar ad shi ne cikin kwanaki uku, daga nan kuma sai a sanar ad sunayen wadanda suka lashe gasara  mataki na farko da kuma na biyu da kuma na uku, tare da basu kyautuka.

An raba gasar ne zuwa bangarori daban-daban, da suka hada da harda da kuma tiilawa, kamar yadda kuma akwai bangaren tafsiri da kuma tajwidi gami da sauran ilmomin kur’ani mai tsarki.

 

3840846

 

 

captcha