Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya habarta cewa, a karon mahukuntan kasar Masar sun bar masu yawon bude sun ziyarci makabartar da ta yi shekaru dubu 4 da ginawa, inda aka bizne daya daga cikin na hannun damar Fir’ana mai suna Mihu a kusa da garin Jiza.
An gano wannan makabarta nea cikin shekara ta 1940, a lokacin Zaki Sa’ad, kuma daga lokacin aka shiga bincike a kanta, inda aka gano wasu zane-zane da suke nuni da irin al’adu na lokacin Fir’auna.
Masar ta bude wannan wuri ne domin ta kara samun kudaden shiga daga masu yawon bude daga kasashen duniya.