IQNA

Baje Kolin Rubuce-Rubucen Kur’ani Na Iran A China

23:54 - June 06, 2016
Lambar Labari: 3480484
Bangaren kasa da kasa, an bude wani baje koli na kur’ani na Iran a birnin Shanghai na kasar China.

Behnam Azad babban jami’I maikula da harkokin al’adu na kasar Iran a Shanghai a zantawarsa da kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa,sun bude wannan baje koli ne da nufin kara yada ayyukan kur’ani a tsakanin al’ummomi musamman ma musulmi a duk inda suke.

Ya kara da cewa wannan baje koli ya kunshi wasu daga cikin kwafin kur’ani da suke dauke da rubutu n musamman, kamar yadda kuma an nuna wasu daga cikin alluna wadanda suke dauke da ayoyin kur’ani mai tsarki da aka kawata rubutunsu.

Baya ga haka kuma an nuna wasu kwafin kur’anai da aka tarjama a cikin harsunan turancin ingilishi da kuma harshe china.

Baje kolin ya samu karbuwa daga mabiya addinin muslunci da suke zaunea wannan birni, har da wasu wadanda ba musulmi,wadanda suke zuwa suna duba a bin da aka ajiye a wurin.

Mujtaba Muhammad Beigi makarancin kur’ani dan kasar zai kasance yana halartar babban masallaci birnin daga ranar 17 zuwa 23 ga wannan wata na Ramadan yana gabatar da karatun kur’ani.

Wannan makarancin kur’ani dan kasar Iran ya saba gabatar da karatu da sautinsa mai kyau a masallacin abayan Magariba a cikin watan azumi.

3504284

captcha