BKamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, wannan gasa ta shafi maza ne zalla, kuma lokacin gudanar da gasar shi ne kamar haka: 19 zuwa 26 ga watan Afirilu 2017.
Ga bayani danganeda gasar ga wadanda suke son su halarta
Bangarorin gasar:
- Hardar dukkanin kur'ani mai tsarki
- Karatun kur'ani mai tsarki
Sharuddan wanda zai halarci gasar:
1 – Zama cikakken dan kasa daga kasar da mutum zai zo
2 – Wanda zai halarta, ya zama bai halarci gasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata a kasar Iran ba
3 – Ya zama yana iya yin karatun kur'ani tare da kiyaye dukkanin ka'idoji da hukunce-hukunce na tajwidi da kyakkyawan sauti
4 – Wanda zai halarta, bangare daya ne kawai na gasar zai iya shiga
5 – Daga kowace kasa mutum daya ne kawai zai iya raka masu shiga gasar
6 – Daukar nauyin VISA, tikitin jirgi da mutum guda dan rakiya, da wurin zama, duk yana kan cibiyar shirya gasar kur’ani
7 – Abubuwan da ake bukata:
Shafin farko na Passpot da ke dauke da hoto da bayanin mutum, kananan hotuna guda 2, tare da form din rijista da mutum ya cika
8 – Wa’adin karshe na karbar wadannan abubuwa:
15 ga Bahman shekara 1395 Shamsiyya, 5 Jumada ula 1438 HJ, wanda ya yi daidai da 3 ga Fabrairun 2017.
9 – Za a iya ziyartar wannan shafi na cibiyar da ke daukar nauyin shirya wannan gasa: www.quraniran.ir
Haka nan kuma za a iya tuntubar wadannan lambobin waya domin neman Karin bayani:
- Wayar salula : 0098 922 3784093
- Layin kasa da Fax: 0098 2164872627
- Adireshin email: awqafiran@yahoo.com
- Hanyar tuntuba ta Telegram da WhatsApp da hanyoyin sada zumunta: 0098 9223784094.