IQNA

Shugaban Iran:

Juyin Juya Halin Muslunci Yana Nan A Raye / Zamu Maida Martani Kan Duk Wani Shishigi

23:44 - February 10, 2017
Lambar Labari: 3481217
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rauhani ya ce har abada Al'ummar kasar Iran ba za su kauce daga hanyar goyon bayan juyin Juya halin musulinci da kuma Jagoran juyin juya halin musulinci gami da gajiyar d Imam Khumaini(k.S) wanda ya kafa Jumhoriyar musulinci ta Iran.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, A yayin da yake gudanar da Jawabinsa gaban milyoyin Jama'a da suka halarci taron tunawa da zagayowar ranar cin nasarar juyin juya halin musulinci a Dandalin 'Yanci dake nan birnin Tehran a wannan Juma'a, Shugaban Kasar ya bayyana cewa Juyin juya halin musulinci da ya wakana a nan kasar Iran shekaru 38 da suka gabata, ya kasance muhimin abu a Tahirin Iran da ya 'yanto kasar daga kangin kasashen waje da Amurka kuma ya canza makomar Al'umma zuwa ga zabinsu.

Dakta Rauhani ya ce Juyin musulinci , shi ne juyi na farko a Duniya wanda kasa da wata biyu Al'umarsa suka kada kuri'a kuma suka zabi tsarin da suke so da kansu.A yayin da ya koma kan irin barazanar da wasu Sabin Shugabanin Duniya musaman ma Shugaban Amurka ke yi kan kasar ta Iran, Dakta Hasan Rauhani ya bayyana cewa wajibi sabin kamu su fahimci cewa idan za a yi magana da Al'ummar Iran to wajibi ne a yita cikin karamci da kuma girmamawa.

Har ila yau Dakta Rauhani ya ce wadanda suke barazana ga Gwamnati gami da Dakarun kasar Iran, kamata ya yi su dauki darasi na gwagwarmaya, juriya, karfi da kuma hadin kai na wannan Babbar Al'ummar, matukar kuma suka kuskure to shakka babu za su fuskanci martani mai girma.

Shugaba Rauhani ya ce Jumhoriyar musulinci ta Iran ba ta neman tashin hankali da ko wata kasa, masu kokarin shafa mata kashin kaji su daina, domin a halin da ake ciki Kasar Iran ta yi karfin da babu wata kasa da za ta yi mata kalon hadarin kaji.

Dakta Rauhani ya kara da cewa bayan juyin musulinci Al'ummar Iran ba ta kauce a kan hanyar tsarin musulinci ba kuma a fagen siyasar kasa da kasar ta canza kalon da ake yima musulinci a matsayin barazana zuwa sulhu.

Ko a jiya a wani zama da masana inda ya gabatar da jawabi ya bayyana cewa yau shekaru talatin da takwas kenan da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, kuma shi ne juyin juya hali mafi muhimmanci a cikin karnin da ya gabata a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya gaba daya. amma a duk tsawon wannan lokacin kasar Iran bata mamaye wata kasa ba kuma bata da niyyan yin haka a gaba.

Amma dangane da ci gaban da kasar take samu a bangaren kere keren makamai kuma shugaban ya bayyana cewa makaman iran gaba daya don kare kai ne, iran ba zata yi amfani da su wajen kaiwa wata kasa hari ba.

3572796


captcha