IQNA

Shugaban Addini A Turkiya:

Hana Kiran Sallah A Quds Hana Gudanbar Da Addinin Muslunci Ne

23:09 - March 10, 2017
Lambar Labari: 3481302
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Gurmaz shugaban cibiyar kula da harkokin muslunci a kasar Turkiya ya bayyana hana kiran sallah a Quds da Isra’ila ta yi a matsayin yunkurin haramta addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin shafaqna cewa, Muhammad Gurmaz ya yi kakkausar suka dangane da hana gudanar da ki8ran sallaha birnin Quds.

Ya ce tun kafin wannan lokacin majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kokarin ganin ta kada kuri’a kan wannan batu, amma sakamakon matakan da wasu ‘yan majalisa suka dauka daga bangaren larabawan Isra’ila lamarin ya fuskanci cikas.

A wannan karon gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta shirya lamarin daga wajen ajaliasr, inda kuma ta gabatar da daftarin kudirin da aka amince da shi yau a majalisar, wanda akasarin ‘yan majalisar yahudawa masu tsatsauran ra’ayi.

Malamin ya kara da cewa, hana gudanar da kiran sallaha masallacin Quds mai alfarma, yana a matsayin hana gudanar da lamurran addini ne a birnin da ma sauran dukkanin yaninan Palastinu, domin kuwa masallacin yana a matsayin masallci na uku ga msuulmi bayan masallacin Makkah da Madina masu alfarma.

3582577

captcha