IQNA

Wayar Da Kan Sabbin Musulunta A Faransa Kan Sahihin Muslunci

20:41 - March 11, 2017
Lambar Labari: 3481305
Bangaren kasa da kasa, cibiyar musulmin birnin Bordeaux na kasar Faransa ta dauki nauyin wayar da kan sabbin mulsunta abirnin kan hakikanin muslunci

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na dw cewa, wakilan cibiyar suna ganawa da wadanda suka muslunta ba da jimawa ba, domin yi musu bayani kan hakikanin addinin mulsunci da kuma koyarwarsa.

Fu'ad sandai shi ne shugaban cibiyar, ya bayyana cewa suna ganawa da wadanda suka mulsunta da ma danginsu, domin yi musu bayani kana bin da ake nufi da muslunci, da kuma yadda za su kauce wa fadawa cikin yaudarar wasu masu kiran kansu musulmi, da suke sanya ma sabbin musulunta tsatsauran ra'ayi, daga nan kuma zuwa kungiyoyin 'yan ta'adda.

Ya ce sun fuskanci matsaloli da dama daga masu dauke da akidar wahabiyanci da suke musuluntar da mutane a turai, inda sukan sanya su a kan tafarkin tsatsauran ra'ayi tare nuna musu kisan dan adam da cire musu tausayin dan adam, wanda hakan kan sanya su shiga kungiyoyin ISIS da sauransu, har su tafi wasu kasashe da sunan jihai, alhali ba su ma gama fahimtar addinin da suka karba ba.

Fua'ad ya ce wannan mataki da suka dauka ya yi tasiri, domin kuwa tuni har an fara rudar da wasu da suka muslunta ba da jimawa ba, da ba domin wannan kokarin ba, da tuni sun tafi syria ko Iraki domin kai hare-hare da sunan jihadi.

Babban abin da wannan cibiyar take nuna ma sabbin musluntar dai shi ne, muslunci addinin zaman lafiya da fahimtar juna ne, da girmama dan adam da kare mutuncinsa da rayuwarsa da dukiyarsa, jihadi muslunci yana zuwa ne a matsayin kariyar kai daga masu cutar da musulmi.

3582806
captcha