IQNA

Taron Kur’ani Na Shekara-Shekara A Iraki

23:43 - March 20, 2017
Lambar Labari: 3481330
Bnagaren kasa da kasa, an fara gudanar da taron kur’ani na shekara-shekara a kasar Iraki a garin Diwaniyya tare da halartar baki ‘yan kasashen ketare a lokacin maulidin Sayyidah Zahra (SA).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qaf cewa, an fara gudanar da wannan taro ne bisa kulawar babbar cibiyar Iamm Baqir (AS) kamar yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara.

Daga cikin bakin da su kazoo taro akwai na kasashen Kuwait, Saudiyyah, Bahrain, Iran, Tanzania, Yemen, Pakistan da kuma Birtaniya, kamar yadda a cikin gida kuma daga lardunan najaf, Ziqar, Basarah, Misan, Babul, Muthanni, Wasit da sauransu.

Babbar manufar wannan taro dai ita ce raya lamarin kur’ani mai tsarki, inda akan gabatar da karatun kr’ani wanda fitattun makaranta na kasar da kasashen ketare ke gabatarwa.

Safa ka’abi fitaccen makamarncin kur’ani na lardin Diwaniyya kuma makaranci na kasa da kasa, ya gabatar da karatu, kamar yadda kuma aka gabatar da jawabai, inda Sayyid Hassan hakim, da kuma Mustafa Isawi suka gabatar da lacca.

Daga karshe a taron bude wannan majalisi Natek Zarkani shugaban cibiyar kula da harkokin kur’ani ta kasar Iraki ya gabatar da jawabinsa na rufe taron.

3585316

captcha