Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daren jiya an gudanar da taron bukukuwan shigar sabuwar shekara shamsiyyah da kuma maulidin diyar manzon Allah Fatima (AS) a birnin Istanubl fadar mulkin Turkiya.
Taron dai ya samu halaratr jakadan kasar Iran a Turkiya, kamar yadda kuma da dama daga cikin Iraniyawa mazauana kasar ta Turkiya suka halarci wurin, gami da jama’ar gari da suke da shawa’ar halartar wannan taro.
An gabatar da jawabi da kuma wakoki na bege, da kuma masu dangantaka da shiga sabuwar shekara ta hijira shamsiyya a wurin.
A kowace shekara dai ana gudanar da bukukuwan shiga sabuwa shekara ta hijira shamsiyya akasashen Iran da kuma sauran kasashen da ske Magana da harshen farisanci, da kuma kasashen da suka hada al’adu iri daya.