IQNA

Farashin Kur'ani Mai Kala Ya Tashi A Masar

23:50 - April 16, 2017
Lambar Labari: 3481412
Bangaren kasa da kasa, tun bayan da cibiyar Azhar ta sanar d hana sayar da kur'ani mai launuka, farashinsa ya tashi a kasuwannin sayar da littafai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin albawwaba cewa, sakamakon matakin da cibiyar ta Azahar ta dauka a watannin baya, a halin yanzu kwafin kur'ani mai launuka ya rubanya a kan farshnsa na lokutan baya, sakamakon hana sayar da shia kasuwanni.

Bayanin ya ce akwai wadannan kur'anai masu tarin yawa a hanun masu sayar da su, amma kuma suna sayar da su ne a boye, duk kuwa da cewa mutane da dama sun bukatar irinsu saboda dadin karatu da kuma banbancen abubuwa da dama da suka shafi rubutu, amma ba asayar da sua bayyane, saboda Azhar ta haramta.

Wasu daga cikin malaman Azhar suka yanke wanann hukunci wanda babu wanda zai iya tayar da shi, kasantuwar cibiyar Azhar it ace cibiyar addini mafi girma a kasar masar, wadda ake komawa zuwa agareta acikin dukkanin wani lamari da ya danganci addinin muslunci.

A cikin 'yan kwanakin nan an kama wasu amsu sayar da kur'ani wadanda 'yan kasar Sudan ne da suke cinikinsa a kan tituna, sakamakon sayar da kur'anai da suke yi ta hanyar wasu mutane a bayan fage, wanda ake ganin hakan ya saawa wanann doka.

3590062
captcha