IQNA

Mai Gabatar Da Shiri A tashar Fox News Ya Ci Zarafin Muslunci

22:07 - April 18, 2017
Lambar Labari: 3481418
Bangaren kasa da kasa, John Scott mai gabatar da shirin fox and friend a tashar fox ya yi batunci da cin zarafi ga muslunci.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin salon cewa, mai gabatar da shirin na tashar fox news ya yi cin zarafin ne ga musluncin alokacin gabatar da shirin nasa.

A lokacin da yake zantawa da wani fitaccen mai shirya fina-finai wanda ya yi shirin fim mai suna kyamar muslunci, wanda a cikinsa ya fito musulmi wanda ake nuna masa kyama a cikin jama'a a cikin kasashen turai.

Mai gabatar da shirin John Scott ya bayyana abin da wannan dan fim din ya yi tamkar wani abun ban mamaki, domin a mahangarsa mutane suna da gaskiya akan yadda suke nuna kyama ga musulmi, saboda hadarin da ke tatatre da msuulmi na ta'adanci.

Amma dan wasan fina-finan wanda shi kansa ba musulmi, ya yi kokarin fahimtar da Scott cewa manufar fim da ya yi ita ce, samar dahanya ta fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, su daina daukar musulmi a matsayin hadari.

Amma Scott ya sheda masa cewa, mun san kana dauke da bama-bamai, idan kana son mu daina daukar musulmi 'yan ta'adda to su daina kasha mutane da kona su da ransu, su daina tayar da bama-bamai suna kashe 'yan adam, furucin da ke ci gaba da fuskantar kakkausar martini daga kungiyoyin kare hakkokin bil adama da dama a nahiyar turai da kuma kasashen musulmi.

3590732
captcha