IQNA

Makaranta Daga Thailand Na Halartar Gasar Kur'ani A Tehran

23:23 - April 20, 2017
Lambar Labari: 3481422
Bangaren kasa da kasa, An shiga rana ta biyu a gasar kur'ani ta duniya da aka bude a jiya a birnin Tehran na kasar Iran a babban dakin taruka da ke babban masalalcin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan gasa da aka bude a jiya, tana samun halartar makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki daga kasashe tamanin da biyu na duniya, da suka hada da kasashen musulmi da na larabawa, da kuma wasu kasashen nahiyar Afirka da na turai da kuma na asia.

Wannan dai shi ne karo na talatin da hudu da ake gudanar da wannan gasa ta duniya a kowace shekara a kasar ta Iran, inda akn dauki kwnaki mako guda ana gudanar da ita.

Gasar dai ta shafi bangarori na harda da kuma kira'a, kamar yadda kuma a kan tabo bangaren hukunce-hukuncen karatun kur'ani da kuma tafsiri, inda daga karshen gasar a kan bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci, da kuma wasu kyautukan na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

A wannan karo dai gasar ta dauki wani sabon salo a karon farko, inda ake gudanar da gasar a bangarori uku, bangaren na farko shi ne na makaranta da mahardata kamar yadda aka saba, sai kuma bangare na biyu shi ne bangaren makaranta da mahardata mata, sai kuma bangaren gasar kur'ani ta nakasassu.

3591334

captcha