IQNA

An Raba Kwafin Kur’ani A Los Angeles A Amurka

23:26 - April 23, 2017
Lambar Labari: 3481433
Bangaren kasa da kasa, an raba kwafin kur’ani mai tsarki a taron baje kolin littafai na birnin Los Angeles na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jaridar Los Angeles Times ta bayar da rahoton cewa, wurin da aka kebance domin nuna littafan muslunci na daga wurin wuraren da suka fi daukar hankali a baki dayan wannan baje koli.

Albort Tampy shi ne mai kula da rumfar da aka kebe domin nuna liffan muslunci a wannan babban baje kolin littafai na duniya a birnin Los Angeles, wanda ya bayyana cewa tun kimanin shekaru da suka wuce ne aka fara kebance wata rumfa ta musamman domin nuna littafan musulunci, amma a wannan karon abin ya fi daukar hankali matuka.

Ya ce wasu cibiyoyin musulmi sun bayar da kyautar kwafin kur’ani guda dubu biyu da aka tarjama a cikin harshen turancin ingilishi da aka raba wa jama’a a wurin, da nufin bayar da dama ga jama’a domin su karanta kur’ani da kansu, domin ganin abin da ya kunsa, sakamakon irin mummunar fahimtar da mutane da dama suke da ita a kan kur’ani.

A jiya Lahadi ne dai aka kawo karshen wannan taron baje koli na birnin Los Angeles na kasar Amurka.

3592313


captcha