IQNA

Isamati Ya Bayyana Cewa:

An Gudanar Da Zaman Taron Sufaye Na Hadin Gwiwa A Senegal

23:19 - May 16, 2017
Lambar Labari: 3481520
Bangaren kasa da kasa, shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal ya bayyana cewa an gudanar da taron hadin gwiwa kan matayin Alhul bait (AS) na sufaye.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun usl;unci a jamhuriyar muslunci ta Iran cewa, bisa irin matsayin da Ahlul bait (AS) suke da shia wurin masu bin tafarkin sufanci a kasar Senegal da suka hada da darikar Tijjaniya, hakan ya sanya an gudanar da taron hadin gwiwa akan mtsayin ahlul bait (AS).

Sayyid Hasan Ismati shugaban ofishin raya al’adu na jamhuriyar muslunci ta Iran a kasar Senegal wanda ya halarci wurin taron ya bayyana cewa, ko shakka babu al’ummar Senegal al’umma ce mai tsananin kauna ga ahlul bait (AS) wanda hakan ne ma ya sanya mafi yawan al’ummar kasar suna bin tafarkin darikun sufanci ne, wanda km hakan yana komawa ne ga tarbiya ta ahlul bait.

Ya ce Iran za ta ci gaba da karfafa gwiwar jama’a da manyan malamai na kasar wajen bunkasa tarukan ahlul bait (AS) a kasar, a karkashin jagorancin manyan malaman dariku na kasar.

Shi ma a nasa bangaren Abdu Ambub mai baiwa shugaban kasar shawara kan addini da ya halarci wurin, yay aba da iorin kokarin da yace Iran nay i wajen hada kan al’ummar msuulmi a kasar da ma sauran kasashen duniya.

3600238


captcha