Masallacin Ahmad Qadiruv Chechniya
Masallacin Ahmad Qadiruv da ke a Grozni babban birnin Chechniya, daya ne daga cikin manyan masallatai na Rasha. An gina shi bisa tsarin masallacin Soltan Ahmad Istanbul, an bude shi ne a watan Mehr na 1387 (shamsiya) tare da halartar Vladimir Putin fira ministan Rasha na lokacin.