IQNA

Musulmin Barcelona Sun Yi Gangamin in Allah Wadai da Ta’addanci

23:56 - August 22, 2017
Lambar Labari: 3481823
Bangaren kasa da kasa, daruruwan musulmi a birnin Barcelona na kasar Spain sun sake yin wani gangamin na yin Allah wadai da ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jaridar Daily Mail cewa, wannan zanga-zanga ta hada dukkanin bangarori na msuulm mazauna birnin.

A yayin jerin gwanon, musulmin sun rika rera taken yin tir da Allah wadai da harin da aka kai a birnin, tare da bayyana hakan a matsayin aikin ta’addanci da ba shi da wata alaka da addinin muslunci.

Kamr yadda kuma suka nuna jiyayinsu ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su, musamman wadanda suka rasa rayukansu da uma wadanda suka samu raunuka.

A ranar Ahamis da ta gabata ce dai wani matashi dan asalin kasar Morocco ya kai hari da mota inda ya taka mutae tare da kashe wasu iamnin sha uku da kuma jikkata wasu fiye da dari.

Bayan hakan kuma ya fice daga motar ya tsere, amma daga bisani an gano matashin mai suna Yunus Abu Ya’akub dan shekaru 22 da haihuwa a wani wuri da ya boye a wajen birnin an Barclona, inda bayan dauki ba dadi daga karshe dai aka halaka shi.

3633157

تظاهرات مسلمانان بارسلون

تظاهرات مسلمانان بارسلون

تظاهرات مسلمانان بارسلون


تظاهرات مسلمانان بارسلون

تظاهرات مسلمانان بارسلون

تظاهرات مسلمانان بارسلون


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha