IQNA

Kyautar Fan Miliyan Daya A Gasar Kur'ani ta Masar

16:33 - October 04, 2017
Lambar Labari: 3481965
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa ta saka lada ta kimanin fan miliyan guda ga wadanda suka nuna kwazo a gasar kur'ani ta share fage.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayayr da rahoton cewa, shafin yada labarai Alwafd ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ta fitar ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa ta saka lada ta kimanin fan miliyan guda ga wadanda suka nuna kwazo a gasar kur'ani ta share fagen gasar duniya a kasar.

Wannan shiri dai ya hada yankuna da dama akasar ta Masar da suka kai kimanin saba'in, inda ake gudanar da gasar ta share fage a dukkanin bangarori, da suka hada da harda da kuma tilawa sai kuma bangaren tajwidi da kuma tafsiri.

Dukkanin wannan shiri dai yana zuwa domin zama cikin shirin fuskantar gasar kur'ani ta duniya da za agudanar a kasar ta Masar, inda wadanda suka fi nuna kwazo ne za su wakilci kasar a wannan gasa.

An kafa sharudda ya zama wajibi dukkanin wadanda za su shiga gasar su zama sun cika su kafin lamunce musu shiga gasar, da hakan ya hada da cewa dole ne mai shiga gasar shekarunsa su zama basu haura talatin da daya ba.

Haka nan kuam daga cikin sharuddan akwai batun cewa mai shiga gasar kada ya zama daya daga cikin malaman kur'ani ko malamai masu wa'azi na kasar, kamar yadda kuma kada ya zama daga cikin wani kwamiti na masu kula da ayyukan kur'ani a kasar.

3649074


captcha