IQNA

A Ganawa Da Shugaban Turkiya Jagora Ya Bayyana Cewa:

Samar Da Wata Sabuwar Isra’ila Manuface Ta Kasashen Yammaci

23:21 - October 05, 2017
Lambar Labari: 3481968
Bangaren siyasa, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya fayyace cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana kokarin sake samar da wata sabuwar Isra'ila ce a yankin gabas ta tsakiya, don haka take ingiza Kurdawa kan raba kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, A ganawarsa da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan a cikin daren jiya Laraba: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Sayyid Ayatullahi Ali Khamene'i ya fayyace irin amfanin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila zasu samu a matakin da 'yan kabilar Kurdawan Iraki suka dauka na gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan neman ballewa daga kasar Iraki domin kafa kasarsu ta Kurdawa; Yana mai jaddada cewa; A fili yake Amurka da sauran manyan kasashen duniya ba wadanda za a dogaro da su ba ne, kuma suke kulla makircin samar da wata sabuwar haramtacciyar kasar Isra'ila a wannan yanki.

Ayatullahi Khamene'i ya kara da cewa: Gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a a yankin Kurdawan kasar Iraki, wata cin amana ce a yankin tare da barazana a nan gaba, don haka Jagoran Juyin Juya Halin na Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne a kan Iran da Turkiyya su dauki matakin kalubalantar wannan masifa ta hanyar bin duk matakan da suka dace, kamar yadda hakki ne a kan gwamnatin Iraki ta kwararan matakai kan wannan babbar barazana.

A nashi bangaren shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya jaddada wajabcin samun hadin kai mai karfi tsakanin Iran da Turkiyya; Yana mai fayyace cewa: Kwararan dalilai da hujjoji suna tabbatar da hannun Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila a batun kokarin raba kasar Iraki, kuma matakin da shugaban yankin Kurdawan Mas'ud Barazani ya dauka na gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan neman ballewar yankinsu, kuskure mai girma da ya tafka kuma babu dalilin da zai sanya a yafe masa.

3649419


captcha