IQNA

23:59 - October 06, 2017
Lambar Labari: 3481973
Bangaren ksa da kasa, akalla mutane 12 ne suka yi shahada a wani harin ta’addanci da aka kai a wani wurin ziyara na ‘yan shi’a a yankina Baluchestan na Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mutane 12 ne suka yi shahada tare da jikkatar mutane 8 a wani harin ta’addanci da aka kai a wani wurin ziyara na ‘yan shi’a a yankina Baluchestan kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar.

Tashar Geonews ta bayar da rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da ake taron ziyara.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na yankin ya sheda cewa, harin na kunar bakin wake ne.

Amwar Alhaq ya ce daga cikin mutane dasuka rasa rayukansu a wurin da wani jami’in ‘yan sanda daga cikin jami’an tsaro da suke aikinsua wurin.

Yanzu haka dai jami’an tsaro sun shiga gudanar da bincike kan lamarin domin gano wadanda suke da hannua cikin lamarin domin daukar atakia kansu.

3649554


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Pakistan ، shahada ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: