IQNA

Masallacin Bedford Ya Tara Taimako Ga Musulmin Rohingya

23:12 - October 07, 2017
Lambar Labari: 3481974
Bangaren kasa da kasa, musulmi a masallacin Bedfor a cikin yankin Tottengham na kasar Birtaniya sun tara taimakon kudi domin bayar da su ga masu gudun hijira 'yan kabalir Rohingya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na bedfordtoday cewa, an tara kudu da suka kai kimanin fan dubu 3 da 646 domin sayen ruwan sha ga 'yan kabilar Rohingya.

Mai Magana da yawun masallacin ya bayyana cewa, sun yanke wannan shawara ne bayan da suka ga ya kamata su tara wani abu domin bayarwa amatsayin taimako ga wadannan bayin Allah.

Yanzu haka dai akwai wasu daga cikin 'yan kabilar Rohingy ada suke cikin mawuyacin hali saboda matsaloli da aka saka su a ciki.

Bisa ga rahotannin da aka fitar, yanzu akwai kananan yara 1400 da suke watangaririya a kan iyakokin Myanmar, sakamakon mutuwar iyayensu ko bacewarsu a cikin ruwa ko kuma an halaka su.

3649985


captcha