IQNA

Taron Cin Abinci A Birtaniya Domin Taimakon ‘Yan Rohingya

23:41 - October 12, 2017
Lambar Labari: 3481993
Bangaren kasa da kasa, wani dakin cin abinci a birnin Thestar na kasar Birtaniya zai dauki nauyin shrya cin abinci domin hada taimako ga mutanen Rohingya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na thestar cewa, wani bababn dakin cin abinci birnin Thestar na kasar Birtaniya zai dauki nauyin shrya cin abinci domin hada taimako ga mutanen Rohingya inda za a sayar da kowane kanon abinci guda akan fan 16,95.

Wannan taimako za a hada shi domin samar da wasu daga cikin abubuwan da ‘yan gudun hijira na Rohigya suke da matukar bukatarsu, kamar rwan sha mai tsafta da kuma wasu abubuwan ci na gaggawa.

Wasu daga cikin dakunan cin abinci na birnin na musulmi da ma wadada ba na musulmi ba, sun ce za su koyi da wannan aiki na alkhairi, domin taimaka ma wadannan bayin Allah.

Shirin ya samu karbuwa matka, ta yadda hakan zai bayar da taimakon gagawa gay an gudun hijirar, wadanda ske cikin mawuyacin hali, wadanda kasashen musulmi suka yi gum da bakunansu kan halin da suke ciki in banda ‘yan kalilan daga cikinsu.

3652074


captcha