IQNA

An Fara Gudanar da Gasar Kur'ani Ta Duniya A Qatar

22:29 - October 23, 2017
Lambar Labari: 3482030
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani ta duniya a kasar Qatar mai taken Tijan Nur.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na panet.co.il cewa, a jiya an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani ta duniya a kasar Qatar mai taken Tijan Nur tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa gasa tana daga cikin manyan tarukan gasa na duniya da ake gudanarwa a bangaren kur'ani tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya.

Daga cikin kasashen ad suke halartar gasar akwai kasashen msuulmi da suka hada da na larabawa da kuma wadanda ban a larabawa ba, da suka hada da na asia da kuma na turai.

Babban kwamitin kula da harkokin kur'ani karkashin ma'aikatar kula da harkokin addinai ta kasar shi ne ya dauki nauyin shirya wannan kamar kowace shekara.

Yanzu haka dai dukkanin wadanda suka karba goron gayyata na wannan gasa sun isa kuma tuni sun fara share fagen gasar ta hanyar karawa da juna.

Za a ci gaba da gudanar da gasar tsawon mako guda, inda daga karshe za a kai ga matakin kusa da na karashe kafin zuwa na karshe, inda za a fitar da matsayi na daya zuwa na biyu da na uku.

3655576


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha