IQNA

Jagoran Kiristocin Lebanon: Ta’addanci Ba Shi Da Wata Alaka Da Musulunci

22:31 - October 23, 2017
Lambar Labari: 3482031
Bangaren kasa da kasa, Bushara Rai jagoran kiristocin Marunia a Lebanon ya bayyana cewa, addinin muslunci ba shi da wata alaka da ‘yan ta’adda ko ayukan ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake jawabi a gaban kiristocin Marunia a garin Salt Lake na jahar Utha a a kasar Amurka, Bushara Rai jagoran kiristocin Marunia a Lebanon ya bayyana cewa, rasin adalci ne a danganta musulunci da ta’addanci, domin kuwa addinin muslunci ba shi da wata alaka da ‘yan ta’adda ko ayukan ta’addanci da wasu ke akatawa.

Ya ci gaba da cewa, akwai wasu daga cikin musulmi da suke fakewa da rigar musulunci suna aikata ta’addanci, amma a lokaci guda basu wakiltar musulmi, domin musulmi kansu basu yarda da haka saboda addinin bai halasta a kasha mutane ba gaira a sabar ba.

A kan ya ce abin da ke muhimamnci shi ne, musulmi da kirista su kara hada kai domin su fuskanci barazanar da ke gabansu, musamman a yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce fiye da shekaru 1300 musulmi da kistoci suna rayuwa a cikin yankin gabas ta tsakiya lami lafiya, amma yanzu wasu masu mummunar akida suna son su rarraba su, kuma bai kamata su yi nasara ba, domin kuwa wadannan makiyan musulmi da kiristoci ne baki daya, kuma ba addini ne a gabansu ba.

3655781


captcha