Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arabi 21 cewa, wannan bayahude ya bayyana cewa sun jima suna gudanar da wannan aikia cikin nahiyar Afirka.
Ya ci gaba da cewa, sayar da makamai yana da babar riba ga Isra'ila a dukkanin bangarori, kamar yadda kuma yake da muhimmanci a gare ta a siyasance.
Haka nan kuma ya yi isahara da cewa, cinikin makaman yakan shafi wasu gwamnatoci da kuma wasu kungiyoyin da suke fafutuka, daga ciki kuwa har da kasar Sudan ta kudu, inda suke sayar da makamai ga gwamnati da kuma wasu kungiyoyi a kasar.
Wannan malamin yahudawa ya kara da cewa, suna shirin ci gaba da kara fadada wanann kasuwanci na makamai a cikin nahiyar Afirka, inda lamarin zai hada da wasu kasashen da ba su shiga cikin shirin ba a lokutan baya.
Abin tuni dais hi ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta jima tana sayar da makamai a cikin nahiyar Afirka, musamman ma ga kungiyoyin da suke tayar da kayar baya ga gwamnatoci a cikin kasashensu.