IQNA

Bayan Kwashe Shekaru Fiye Da Biyu A Tsare Sheikh Zakzaky Ya Gana Da ‘Yan Jarida

23:37 - January 13, 2018
Lambar Labari: 3482293
Bangaren kasa da kasa, bayan kwashe tsawon shekaru fiye da biyu yana tsare Sheikh Ibrahim Zakzaky Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya gana da wasu ‘yan jarida da jami'an tsaro suna gayyata.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga wasu kafofin yada labara a Najeriya cewa, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gana da manema labarai ne bayan kwashe da aka kai shi asibiti domin duba lafiyarsa a birnin Abuja.

Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da likitocinsa suke duba shi tun bayan kamun da aka yi masa, inda likitan jami’an tsaro ne kawai yake duba shi tsawon lokacin da ake tsare da shi.

Sa’annan kuma ya yi godiya dangane da irin addu’oin jama’a, inda daga nan kuma sai aka yanke bidiyon.

A cikin ‘yan kwanakin nan dai an gudanar da jerin gwano da gangami a birane daban-daban a Najeriya, domin neman a saki Sheikh Zakzaky, musamman ma domin samun damar duba lafiyarsa.

3681641

 

captcha