IQNA

Daruruwan ‘yan kasashen Waje Na Samu Horo Kan ilmomin Kur’ani A Najaf

22:35 - March 02, 2018
Lambar Labari: 3482444
Bangaren kasa da kasa, daruruwan ‘yan kasashen ketare ne ke ci gaba da halartar wani shirin bayar da horo da aka bude a birnin Najaf na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, yanzu haka daruruwan ‘yan kasashen ketare ne ke ci gaba da halartar wani shirin bayar da horo da aka bude a birnin Najaf a cibiyar kur’ani ta haramin alawi.

Bayanin ya ce wannan shirin cibiyar raya ayyukan kur’ani ta Imam Ali (AS) ce ta dauki nauyin shirya shi da kuma gudanar da shi.

Sheikh Muhammad Fakhruddin shi ne babban darakta na wannan cibiya, ya bayyana cewa yanzu haka ron sun fito daga kasashe daban-daban, da suka hada da Pakistan, Afghanista, Azarbaijan, Turkiya da kuma kasashen Afrika.

Daga cikin abubuwan da suke samun horo a kansu akwai ilmomin kur’ani mai tsarki, da suka hada kira’a, sanin hukuncin karatu, bayanai kan ayoyi da makamantan hakan, da koyar da su darussa na Nahjul balagha da sahifa sajjadiyya.

3696001

 

 

captcha