Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Riyad ta bayar da rahoton cewa, bayan wata shawara da wasu ‘yan majalisa su 25 suka bayar kan a rika jinkirta lokacin kiran sallar Isha’i majalisar kasar Saudiyya za ta yi dubi kan wannan batu.
Shawar dai tana magana ne kan a rika jinkirat kiran sallar isha’i e har zuwa saoi biyu bayan kammala magariba, musamman a manyan birane, sakamakon yadda hakan yakan saka ‘yan kasuwa cikin gaggawa a lamrinsu saboda lokacin yana kure musu.
Wannan yazo bayan umarnin da yariman saudiyya saurayi mai jiran gado ya bayar e, kan cewa adaina takura ma ‘yan kasuwa kan rufe shagunansu a lokacin salla.