IQNA

Bikin Yaye Daliban Jami'ar Musulunci A Kasar Ghana

23:39 - April 08, 2018
Lambar Labari: 3482550
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron bikin yaye dalibai na jami'ar musulunci ta Umma a kasar Ghana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama'a na cibiyar yada ala'dun musulunci ya gabarta cewa, an bude wannan jami'a ne tun a cikin shekara ta 1997 a matsayin kwalejin koyon ilmomin addinin muslunci.

A wurin bukin an yaye dalibai 449 maza, sai kuma wasu 390 mata, 127 a matakin karatu na digiri, yayin da kuma a matakin karatu na diploma.

Bangarorin da suka kamala karatu a bangarensu kuwa sun hada da ilimin kasuwanci, ilimin sanin kwamfuta, shari'ar musulunci, nazari kan ilmomin musulunci, sanin harkokin kudi da banki a mahangar musulunci, sai kuma harshen larabci.

Abdulgafur Busa'idi mataimakin shugaban jami'ar ya gabatar da jawabi, inda ya ce akwai bukatar kara habbaka matsayin karatun jami'ar, ya zama daga digiri na farko zuwa abin da ya yi sama.

3703532

 

 

 

 

 

captcha