Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau an dauki Ayatollah Sheikh Isa Qasem daga asibiti zuwa filin jirgin sama na birnin Manama domin fitar da shi zuwa wajen domin yi masa maganai.
Bayani da kafofin sadarwa na zumunta suke bayarwa daga kasar ta Bahrain na tabbatar da cewa, masarautar kama karya ta kasar ta fitar da babban malamin zuwa wajen kasar.
Masarautar kama karya ta Bahrain ta yanke wanann shawara ne sakamakon kakkausar suka da take fuskata daga dukkanin kungiyoyi da cibiyoyi na kare hakkin bil adama na duniya kan yadda suke cutar da wannan malami mai kira zuwa ga zaman lafiya da adalci a kasar.